Cire T-Gwarzo Daga Minista Babban Kuskure ne – Kungiya Matasan APC ta Kasa

Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta kasa ta kalubalanci tsige Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo a matsayin karamin ministan gidaje da raya birane.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da shugabanta Abdullahi Wada Kura ya sanyawa hannu kuma ta aikowa kadaura24, ta bayyana cire Gwarzo a matsayin abin mamaki da hadari ga jam’iyyar APC a jihar.

“Mafi yawan al’ummar jihar Kano sun tausayawa sakamakon cirewar da aka yi masa. Cire shi daga minista ya haifar da rashin jin dadi kuma zai kawo tsaiko ga tasirin jam’iyyar APC a jihar Kano,” a cewar kungiyar.

T Gwarzo wanda aka tsige shi da wasu mutane 4 ya godewa shugaban kasar da ya bashi damar yiwa kasarsa hidima.

Kungiyar ta yi zargin cewa wani fitaccen dan Siyasa daga jihar kano ne ya kitsa yadda aka cire T Gwarzo daga Minista.

“Wanda ya kitsa cireT Gwarzo ya yaudari shugaban kasa, kuma ya kamata ya sani mutum daya bai isa ya rika yanke shawara da sunan Kano ba,” inji kungiyar

Kungiyar ta yi gargadin cewa wannan mataki kokari ne kawai na karawa jam’iyyar NNPP karfi cikin dubarane, ganin cewa bai kamata a jefar da ’yan siyasa irinsu Gwarzo ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

“Idan ba a mayar da shi Kan mukaminda ba, nan da shekarar 2027, shugaban kasa zai gane ko Gwarzo na jama’a ko ba shi da su, amma ta fito filin cewa al’ummar jihar Kano suna tare da Gwarzo saboda yadda jam’a suka tausaya masa .

“Kano ta Arewa ta zamo babbar shiyyar APC ce saboda yadda Gwarzo da sauran masu ruwa da tsaki suka fito daga shiyyar, ba wai don mutum daya ba.

Ya kamata shugaban kasa ya duba amma matakin da aka dauka shawara ce mai hadari a 2027,”in ji Wanda.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 7 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 49 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com