Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jiragen samanta sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a ranar 25 ga Oktoba a arin Bula Marwa a Borno.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Iya Comodore, Olusola Akinboyewa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Akinboyewa ya ce sun gano Bula Marwa ne garin da Boko Haram suka taruwa, inda suka gano babura suna ta zirga-zirga, hakan ya sa aka aika jiragen sama yankin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Da isan jiragen, sai hoton da jiragen ya ɗauko ya tabbatar da taron ƴan Boko Haram a saman babura 12, inda aka bibiyi baburan zuwa wani wuri da akwai ƙarin ƴan ta’addan suke jiran zuwan su.
“Wannan ya sa jiragen suka yi ɓarin wuta a yankin, sannan daga baya jirgin ya hango ƴan ta’addan suna sake dawowa yankin domin kwashe waɗanda suka raunata.
“Wannan ya sa jiragen suka koma, suka ƙara yin luguden wuta, inda a nan ma aka sake kashe wasu ƴan ta’addan.”
Akinboyewa ya ce an sake ganin wasu tarin ƴan Boko Haram sun taru a ƙarƙashin wata bishiya, inda nan ma jiragen suka ƙara bin su, suka musu ɓarin wuta.











