NNPLC ya sake kara farashin Man Fetur a Najeriya

A karo na biyu kamfanin man Fetur na Nijeriya ya sake kara kudin Man abin da ya haifar da kace nace da mamaki bayan karin da yazo a ba zata ranar Talata 29 ga Oktoba 2024, wanda wannan shine Karo na biyu da kamfanin yayi ƙari cikin makonni uku.

Kamfanin man na kasa ya kara farashin daga naira 1,030 zuwa 1060 a Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da a Jihar Legas farashin ya koma Naira 1,025 daga 998 a kowacce lita.

Kafin wannan ƙarin, ana sayar da litar man fetur ne a  kan N897 a Abuja, a Legas kuma N885, amma a ranar 9 ga watan Oktoba da muke bankwana da shi aka ƙara na Legas zuwa N998, na Abuja kuma zuwa N1,030.

Ķarin kudin na zuwa ne duk da fara aikin Matatar Man Ɗangote, wadda ake tunanin za ta kawo sauki da wadatuwar man a ƙasar.

Tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye Tallafin mai a watan mayun 2023, NNPCL ya ƙara kudin fetir daga 184 zuwa 1,025 a Jihar Legas.

Masana dai na ganin wannan wani mataki ne da zai kara jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali, dama tuni wasu suka ajiye ababen hawan su saboda tsadar farashin man.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 32 minutes 36 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 14 minutes 1 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com