Jam’iyyun siyasa da ‘yan takara sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
An yi bikin sanya hannun ne ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na ƙasa NPC, a cibiyar raya al’adu da ke Akure, babban birni jihar.
Shugaban kwamitin, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga duka masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyu da ‘yan takara su amince da sakamakon zaɓen matsawar an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana.
A nasa ɓangare shugaban hukumar zaɓen kasar, Farfesa Mahmood Yakubu ya yaba wa kwamitin bisa ƙoƙarinsa na haɗa kan jam’iyyun da ‘yan takara a teburin yarjejeniyar zaman lafiya a lokutan zaɓukan ƙasar.
Farfesa Yakubu ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da sarakuna da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa hannu da hukumarsa don gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin kwanciyar hankali da lumana.
A ranar 16 ga watan Nuwamban da muke ciki ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar ta Ondo.











