Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce kashi 85 cikin 100 na al’ummar jihar Ondo sun karɓi katin zaɓensu, yayin da ya rage mako gudanar da gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
Cikin wani saƙo da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na X, ya nuna cewa mutum 2,053,61 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
INEC ɗin ta kuma ce mutum 1,757,205, wato kashi 85 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar ne suka karɓi katin zaɓen nasu, yayin da mutum 295,856 suka gaza karɓar katunan nasu.
Tuni dai hukumar zaɓen ta fara horas da masu aikin zaɓe na wucin gadi da za su jagoranci gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓen jihar.











