Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben jihar Ondo, bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben.
PDP ta ce za ta garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.
Muƙaddashin hulda da manema labarai na Jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa an tafka magudi da amfani da karfin tsiya aka kada dan takararsu Mr. Agboola Ajayi.
Read Also:
Hakan na zuwa ne bayan wasu korafe-korafe da wakilin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Idanre ya yi zargin cewa ba a yi zabe a unguwar Ofosun Oniseri ba, yayin da aka kori ƴan PDP, aka ƙwace ƙuri’u a Alade.
Alhaji Abdullahi Ibrahim ya yi zargin cewa zaben ya saɓa wa tsarin dimokuradiyya inda ya ce za su dauki mataki na gaba.
“Za mu garzaya kotu a matsayinmu na jam’iya, da muke sukar lamirin wannan zaɓe, mun yi tir da Allah wadai da hukuncin da hukumar zaɓe ta bayar.”
Tuni jam’iyyar PDP ta ce za ta yi nazari kan zaben da kuma sakamakonsa kafin ɗaukar mataki na gaba kan abin da ta kira kare dimokuraɗiyya a Najeriya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1250 days 57 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1232 days 2 hours 39 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com