Majalisar dattawan Najeriya ta amince a haramta wa duk wani ɗan ƙasar da aka samu da aikata laifi a ƙasashen waje, yin amfani da fasfon Najeriya na tsawon shekara 10.
Majalisar ta amince da hakan ne a yayin zaman da ta yi a Abuja, a ranar Talata
Sanata Abubakar Bello mai wakiltar jihar Neja ta arewa ne ya gabatar da ƙudurin a gaban majalisar, a wani ɓangare na yi wa dokar fasfo ɗin garambawul.
Ƙudurin ya buƙaci a karɓe fasfo ɗin ne na tsawon shekara 10 mafi ƙaranci, abun da suke ganin zai taimaka wajen sanya ƴanƙasar da ke waje kuma suke aikata manyan laifuka shiga taitayinsu.
Ƴan majalisar na fatan matakin zai taimaka wajen magance ɓata sunan ƙasar da wasu ke yi a ƙasashen ƙetare.