Haɗakar kwamitin majalisar dattawa da ta wakilan tarayya mai duba batun gyaran kundin tsarin mulki ta amince da ƙirƙirar sabbin jihohi guda shida a Najeriya.
Wannan mataki ya biyo bayan taron ƙara wa juna sani na kwanaki biyu da kwamitin ya gudanar a jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da takwaransa na majalisar wakilai, Benjamin Kalu.
Read Also:
A taron, an tattauna kan buƙatu 69 da suka haɗa da neman kafa sabbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Daga cikin waɗannan buƙatun, kwamitin ya zaɓi amincewa da ƙirƙirar jihohi guda shida — ɗaya daga kowace shiyyar ƙasar — domin tabbatar da daidaito a rabon jihohi.
Idan wannan shawarwarin ya samu amincewar doka, adadin jihohin Najeriya zai karu daga 36 zuwa 42.










