Kungiyar Arewa Connect Movement ta bayyana bakin ciki kan sabon harin da yan bindiga suka kai Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke kauyen Papiri a Karamar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, inda suka yi awon gaba dalibai da ma’aikata da ba a san yawan su ba.
Kungiyar ta ce wannan lamari babban tashin hankali ne ga iyaye, yan uwa da kuma al’ummar kasa baki ɗaya.
Read Also:
A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Auwal Mahmud Durumin Iya, ya fitar, ya bayyana cewa a kwanan nan irin wannan abu ya faru inda aka sace dalibai mata 25 a Jihar Kebbi, kuma har yanzu ba a samu wani cigaba a kan lamarin ba, inda ya ce sake faruwar irin wannan al’amari a cikin lokaci kankani na sake nuna yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan kalubale ne babba ga gwamnati da hukumomin tsaro, tare da kira gare su da su sauya dabarun yaki da yan ta’adda domin kawo karshen wannan ta’asa wacce ta dade tana addabar al’umma.
A karshe, kungiyar ta mika sakon jaje ga Gwamnatin Tarayya, jihohin Neja da Kebbi, iyayen yara, da al’ummar ƙasa baki daya, tana mai rokon ALLAH Ya kawo dauki cikin gaggawa.










