Gwamnan Kano Ya Kafa Runduna ta Musamman Don Tabbatar da Tsaro a Tashoshin Mota

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa Runduna ta Musamman (Special Task Force) domin magance barazanar tsaro a tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a fadin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi. Sanarwar ta ce matakin na nuna kudurin gwamnati na hana kutsen masu aikata laifi, musamman a wuraren shiga da fita na birnin Kano.

An bayyana tashoshin mota a matsayin wuraren da ke da hadarin tsaro, sakamakon yawaitar zirga-zirga da kuma kamun wasu da ake zargi da aikata laifi a tashar mota ta Kofar Ruwa kwanan nan.

Rundunar za ta gudanar da sa ido, tattara bayanan sirri da hadin gwiwar ayyukan tsaro a tashoshin mota, gidajen mai da sauran wuraren jama’a, domin dakile barazana tun kafin ta tsananta. Gwamnan ya jaddada manufar gwamnatinsa ta ba da cikakken goyon baya ga hukumomin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com