Tinubu ya maye gurbin Engr Farouk daga shugabancin hukumar NMDPRA

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawar ƙasar ta amince da naɗin Engr Saidu Aliyu Mohammed, a matsayin sabon shugabannin Hukumar Kula da Albakatun mai na kan tudu NMDPRA, bayan murabus daga matsayin da Engr Farouk Ahmed ya yi.

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaban ya kuma nemi majalisar ta amince ya naɗa Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan, a matsayin magajin Gbenga Komolafe, da ke shugabantar hukumar kula da albarkatun mai na cikin ruwa.

Tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari ne ya naɗa su a shekarar 2021, domin jagorantar hukumomin biyu da dokar masana’antar mai ta ƙasar ta ƙirƙiro.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar lahadin da ta gabata, shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya zargin Engr Farouk Ahmed da biya wa ƴaƴansa 4 kuɗin makaranta a Switzerland, da suka kai dala miliya biyar.

Tuni dai hukumar yaƙi da almundahana ta ICPC a Najeriya, ta tabbatar da karɓar ƙorafin da Ɗangote ya shigar gabatanta, kuma ta ce za ta yi bincike akai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com