Gwamnati Nijeriya ta haramta fitar da itace zuwa ƙasashen waje

Gwamnatin Najeriya ta haramta fitar da itace da kayayyakin da suka shafi itace zuwa ƙasashen waje a faɗin ƙasar baki ɗaya, tare da soke dukkan lasisi da izini da aka bayar a baya kan irin wannan kasuwanci.

Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba daga bakin ministan muhalli, Balarabe Lawal, yayin taron malalisar ƙasa kan kare muhalli karo na 18 da aka gudanar a Jihar Katsina.

Balarabe Lawal ya ce wannan umarni na cikin wata sabuwar dokar zartarwa ta shugaban ƙasa wadda aka ɗauka domin dakile sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba da kuma lalacewar gandun daji a sassan ƙasar.

Ministan ya jaddada cewa gandun dajin Najeriya na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar muhalli, domin suna samar da iska da ruwa masu tsafta da tallafa wa hanyoyin samun abin rayuw da, kare nau’o’in halittu, da rage illar sauyin yanayi.

Ya kuma yi gargaɗi cewa ci gaba da fitar da itace zuwa ƙasashen waje na barazana ga waɗannan fa’idodi da kuma lafiyar muhalli a nan gaba.

Dokar wadda aka fitar ta dogara ne da sashe na 17(2) da 20 na ƙundin tsarin mulki na 1999 (da aka yi wa gyara), waɗanda ke bai wa gwamnati ikon kare muhalli da gandun daji da namun daji, tare da hana cin gajiyar albarkatun ƙasa don amfanin ƙashin kai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com