Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, yana mai danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar, tare da cewa ya dauki wannan mataki ne domin kare muradun al’ummar jihar Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya rattaba wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a jihar ranar Juma’a.
A wata wasika da gwamnan ya aike wa shugaban jam’iyyar NNPP na mazabarsa ta Diso-Chiranchi dake Karamar Hukumar Gwale, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tun daga yau Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
A cewar gwamnan, “Na rubuto wannan wasika ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar NNPP matsayina na ficewa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun bayan shigarsa jam’iyyar a shekarar 2022.
Read Also:
Gwamnan ya ce jam’iyyar na fama da rikice-rikicen cikin gida, sakamakon sabanin shugabanci da kuma shari’o’i da dama da ke gaban kotuna a sassa daban-daban na kasar nan.
A cewarsa, wadannan rikice-rikice sun haifar da rarrabuwar kai da raunana dunkulewar jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa bayan yin nazari mai zurfi, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne bisa la’akari da muradun jama’a.
Gwamnan ya jaddada cewa ya dauki matakin ne da kyakkyawar niyya, ba tare da wata gaba ko kiyayya ba, yana mai tabbatar da kudirinsa na ci gaba da wanzar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya fice daga jam’iyyar tare da mambobi 21 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi 8 na Majalisar Wakilai ta kasa, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar.
Sakataren jam’iyyar NNPP na mazabar Diso-Chiranchi, Honarabul Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karbar wasikar ficewar gwamnan, inda ya yaba masa bisa ayyukan raya kasa da ya aiwatar, musamman a bangarorin ababen more rayuwa, gyaran birane, lafiya, ilimi da bunkasa tattalin arziki.












