Gwamnan Kano zai koma Jam’iyyar APC

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na shirin komawa jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, bayan ya fice daga jam’iyyar NNPP a ranar Juma’ar da ta gabata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu kuma aka raba manema labarai ranar Lahadi.

Idan Za a iya tunawa Gwamna Yusuf ya taba shiga jam’iyyar APC ne a shekarar 2014, lokacin da ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar domin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, sai dai daga bisani ya janye wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan shafe shekaru yana harkokin siyasa a jam’iyyu daban-daban, ciki har da NNPP, inda a halin da ake ciki harkokin mulki, haɗin kan ƙasa da kuma buƙatar ci gaba sun sa ya yanke shawarar komawa APC, wadda ya bayyana a matsayin jam’iyya mai tsari da gogewa wajen tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya.

Gwamna Yusuf ya ce komawarsa APC za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya, da kawo ci gana jihar Kano .

Ya ƙara da cewa matakin zai taimaka wajen ƙarfafa kwanciyar hankali da haɗin kan siyasa a jihar.

A ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, ana sa ran gwamnan zai yi rajistar shiga jam’iyyar APC a hukumance a Kano tare da mambobi 22 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi takwas na Majalisar Wakilai da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Haka kuma ana sa ran zai ƙaddamar da shirin rajistar APC ta yanar gizo (e-registration) a faɗin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com