Daga Yushau A. Shuaib
Kisan da aka yi wa Malam Bashar Sani, wani babban jami’i a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Maru, wani abin takaici ne da ke nuna irin kalubalen tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya.
Duk da cewa ‘yan uwan shi sun biya sama da naira miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa tare da bayar da babura, wayoyi da katunan waya duk domin a saki dan uwansa da aka sace tsawon shekaru, a ƙarshe ‘yan bindigar da suka karbi wadannan makudan kudi ne suka kashe shi.
Shekaru da dama, waɗannan ‘yan bindiga suna kai hare-hare ga iyalinsa: sun sace matansa biyu, ƙaninsa, sannan daga baya suka sace shi tare da matarsa da ‘yarsa da wasu maƙwabta. Duk lokacin da hakan ta faru, iyalan suna sayar da kadarorin da suka mallaka gami da neman taimako domin biyan bukatun ‘yan bindigar da kullum ke ƙaruwa.
Ko bayan sun biya naira miliyan 20 tare da ƙarin babura, sai aka ce musu su jira ƙarin umarni. Amma ba tare da saninsu ba, Malam Bashar ya riga ya rasu a hannun ‘yan bindigar sakamakon azabtarwa da raunukan da ba a kula da su ba. Matarsa da ‘yarsa sun dawo gida; shi kuwa bai dawo ba.
Wannan lamari ba shi kaɗai ya shafa ba, ba kuma a kansa farauba. Yana nuna yadda rashin tsaro ke ƙara tsananta a Jihar Zamfara da sauran sassan Arewaci, inda al’umma ke shiga cikin wani Mawuyacin hali na biyan kuɗin fansa, gami da karɓar haraji daga ‘yan bindiga.
A wasu wurare, kauyuka gaba ɗaya sun zama kufai. Wasu kuma suna biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su iya noma, aiki ko kuma su sami kwanciyar hankali da daddare. Iyalan mutane suna jinginar da gidajensu, sayar da dukiyoyinsu, ko neman tallafin jama’a domin ceto ‘yan uwa nsu.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne cewa yawancin masu aikata wannan ta’asa mutane ne da ke magana da harshenmu, suna bin addininmu, kuma kuma al’adunmu daya. Duk da haka suna aikata zalunci da rashin tausayi da ya sabawa Dan Adamtaka. Ba za mu iya ci gaba da cewa wai wasu baƙi ko fatalwowi ne kawai ke aikata hakan ba. Ya zama dole Arewa ta fuskanci wannan Gaskiyar mai daci, mutanenmu na cikin wannan rikici.
A shekarar 2018, na rubuta wata makala mai taken “Still on Murderous Fulani Kidnappers”, inda na yi nazari kan yadda wasu da ake dangantawa da Fulani suka shiga harkar garkuwa da mutane wata sana’a da a baya ake dangantawa da wasu ‘yan bindiga a wasu yankuna.
A wancan lokaci, rahotannin ‘yan sanda sun nuna cewa wasu da aka kama sun amsa aikata fyade, kisa da sauran miyagun laifuka.
Tambayoyin da na yi a lokacin har yanzu suna nan ba su da amsa:
Ta yaya makiyaya suka bar sana’arsu ta gargajiya suka koma garkuwa da mutane? Wa ke ba su makamai na zamani? Me yasa suke kashe mutane ko bayan sun karɓi kuɗin fansa? Ta yaya suka koyi dabarun da suka sa suke aiki kamar sojojin suka sami horo? Kuma mafi muhimmanci, ta yaya gwamnati da al’umma za su haɗa kai su kawo ƙarshen wannan bala’i?
Read Also:
Tun a wani taron ƙasa da ƙasa kan kiwo da aka yi a 2014, an yi gargadin cewa ‘yan ta’adda na iya ɓoye kansu a cikin makiyaya domin amfani da rikicin manoma da makiyaya. An ba da shawarwari na tsaro, amma ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba.
Yanzu rikicin ya wuce rikicin kiwo kawai. Ya zama rikici da ke da nasaba da talauci, gazawar tsarin tsaro, da kuma shigar ƙungiyoyin masu aikata laifi, musamman a wuraren hakar ma’adinai a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Misali, yankin Maru na da ma’adinan zinariya da lithium, wanda ya jawo masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kuma masu aikata laifi.
Ƙirƙirar Federal Ministry of Livestock Development mataki ne mai kyau, amma dole ne a haɗa shi da tsare-tsaren amfani da ƙasa, tantance hanyoyin kiwo, da kuma sabbin hanyoyin kiwo kamar ranching da fasahar sa ido kan dabbobi.
Haka kuma, ya zama dole a ƙarfafa tsaron karkara ta hanyar ‘yan, tsarin gargadin gaggawa, da kuma kula da iyakoki.
Tattaunawa na da muhimmanci, amma yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka yi a baya sau da yawa sun gaza. Don haka dole ne a magance matsalar ‘yan bindiga tun daga tushe: dawo da ikon gwamnati a yankunan karkara, gyara rayuwar waɗanda suka tuba, da kuma rusa hanyoyin biyan kuɗin fansa.
Amma ba gwamnati kaɗai ba ce ke da alhaki. Arewa kanta dole ta farka. Ba wata ƙasa ko wata runduna daga waje da za ta zo ta ceci mu. Da za su iya kare kauyukanmu ko gonakinmu. Wannan alhakin na wuyanmu.
Sarakunan gargajiya, malamai, dattawa, matasa da ƙungiyoyin farar hula dole su haɗa kai domin dawo da tsaro a cikin al’ummarmu. A lokaci guda kuma, dole ne a samawa matasan karkara hanyoyin rayuwa masu kyau kamar horon sana’o’i, rance ga ƙananan sana’o’i, da damar aikin noma.
Arewa ba za ta iya ci gaba da miƙa rayuwarta ga wasu ba. Ba Donald Trump ko wata ƙasa daga waje da za ta zo ta warware wannan matsala.
Ceton Arewa zai fito ne daga Arewa kanta ko kuma a ci gaba da zama a haka.
Dole mu kare al’ummarmu, mu nemi shugabanni da hukumomin tsaro su yi abin da ya dace, kuma mu ƙi miƙa ƙasarmu ga masu laifi da ke magana da harshenmu amma suna cin amanar addininmu da al’adunmu.
A cikin Al-Kur’ani mai girma akwai ayar da ta dace da wannan hali:
Da Allah mahalicci ke cewa“Ku ji tsoron fitina wadda ba za ta shafi waɗanda suka aikata zalunci kawai ba daga cikinku, har da marasa laifi.” (Al-Anfal: 25)
Wannan fitina ta riga ta zo. Idan ba mu haɗa kai muka fuskanci matsalar ‘yan bindiga da gaske ba, wannan tashin hankali zai ci gaba, kuma ya zama karshen rayuwar mutanen da ba su ji ba basu gani ba kamar na Malam Bashar Sani.
Tambayar yanzu ita ce: za mu tashi mu yi wani abu kafin karin rayuka su salwanta?
Makomar mu tana hannun mu.
Kuma lokacin ɗaukar mataki shi ne yanzu.
Yushau A. Shuaib, Marubuci kuma Kwarre a harkar sadarwa, duba www.YAShuaib.com Email: [email protected]












