Home Taska ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai a Jami’ar OOU

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai a Jami’ar OOU

OOU

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Dakunan Kwanan Dalibai a Jami’ar OOU

 

Jihar Ogun, Nigeria – Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOU) da ke Ibogun a jihar Ogun.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bude wuta daga shiga cikin gidan kwanan da tsakar daren jiya Juma’a, lamarin da ya jefa dalibai cikin firgici yayin da suka rika guduwa domin tsira.

Mahara sun bude wuta a dakunan kwana Rahotan jaridar The Nation ya ce harin ya fara ne da tsakar dare, ya kuma ci gaba har zuwa safiyar Asabar, inda sama da mutane 12 dauke da makamai suka shiga dakunan kwanan dalibai da dama.

An ce maharan sun rika harbe-harbe domin tsoratar da dalibai kafin su kwashe wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki masu daraja.

Yadda daliban OOU suka shiga firgici

Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Michael Mabayomije, ya bayyana cewa maharan sun yi aiki na tsawon lokaci ba tare da jami’an tsaro sun kai dauki ba.

Ya ce dalibai da dama sun jikkata a harin, yayin da wasu kuma suka shiga matsanancin firgici saboda tashin hankalin da suka gani.

Jaridar Punch ta kuma rawaito cewa an ga jini a bango da bene na daya daga cikin gidajen kwanan dalibai da abin ya shafa.

Mazauna Ibogun sun bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali, inda suka ce karar bindiga ta karade harabar jami’ar yayin da dalibai ke kokarin tserewa domin ceton rayuwarsu

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun samu raunuka yayin da suke kokarin gudu ko kuma tsayawa kare kansu.

Wane mataki yan sanda suka dauka?

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami’ai suka kaddamar da bincike kan lamarin.

Ya ce an fara bincike kan harin, tare da tura jami’an tsaro ciki har da DPO na yankin Ibogun da kuma kwamandan da ke kula da yankin domin duba halin da ake ciki da kuma kwantar da hankalin dalibai da mazauna yankin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp