Home Taska ɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr...

ɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi 

ɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi 

 

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kamawa da tsare Dr Bashir Kurfi, lamarin da ya biyo bayan jawabin da ya game da matsalolin tsaro.

A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin Trust, Dr Kurfi ya zargi gwamnatin jihar Katsinda da hannu a ɗaukar nauyin ƴanbindiga zuwa Hajji.

A ranar Laraba ne aka gabatar da malamin jami’ar a kotun Majistare a Katsina bayan rundunar ƴansandan jihar ta tuhume shi ƙazafi da ɓata suna.

Alƙalin kotun mai shari’a Zaharaddeen Kofar Soro ne ya buƙaci ƴansanda su cigaba da tsare wanda ake ƙara har zuwa lokacin da za a cigaba da sauraron shari’ar.

Da take jawabi kan batun, Amnesty ta ce Kurfi ya amsa gayyatar ƴansanda ne a ranar Talata 7 ga watan Yuliln 2026 domin amsa tambayoyi, amma a cewar ƙungiyar sai aka faɗa masa cewa za a tsare.

“Yanzu ana ƙoƙarin ganin an tsare shi na tsawon lokaci ta hanyar ƙirƙirar tuhume-tuhume,” in ji ƙungiyar, wanda a cewarta karya ƴancin tofa albarkacin baki ne.

“Gwamnatin jihar Katsina na so ne ta hukunta kawai don ya yi tambayoyi game da yadda take kula da harkokin da suka shafi yaƙi da ƴanbindiga maimakon ta bincika abin da ya faɗa.”

Amnesty ta ce an tsare Kurfi ne domin a tsoratar da mutane su daina tsokaci kan gwamnati. “Bai kamata a hukunta mutum ba domin ya soki gwamnti. Dr Kurfi bai aikata laifin komai ba, kuma tsare shi cin amanar aiki ne domin yana da ƴancin tambaya ko sukar yadda gwamnati take gudanar da aiki.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
https://nnn.ng/image-compressor/
Latest News
Akwai Yiwuwar ba zan kai Lokacin Zaɓen 2027 ba - ObiHukuncin da Kotu ta Yanke wa Direban Keke Napep Kan Aikata Fyaɗeɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar TsaroGwamnatin Tarayya ba ta Yanke Hukuncin Sauya Kayan NYSC ba - Ministan MatasaJuyin Mulki: DSS ta Gurfanar da Mutane 5 kan ɓoye Timipre Sylva Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 Tare da Limami a Jihar Sokoto Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta'addaJami'an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche NnajiYan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar BenueNMDPRA ta Gargaɗi Gidajen Man da ba su Rage Farashi ba NECO: ɗalibai 35 na Hannun Ƴan Bindiga - Ƴan Sanda Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga LegasGwamnatin Najeriya ta ƙudiri Anyiar Tara N2.5trn Daga Kuɗaɗen Shiga a 2026Wanda ya Kafa PRNigeria ya Nufi Kotu Don Daukaka Kara Kan Watsi da Karar ₦1bn da ya Shigar Kan NIPSS
X whatsapp