‘Yan Sanda 4 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Tawagar Motar Ministocin Buhari ta yi Hatsari a Jahar Delta

‘Yan Sanda 4 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Tawagar Motar Ministocin Buhari ta yi Hatsari a Jahar Delta

Daya daga cikin motocin da ke cikin ayarin shugaban ma’aikatan Buhari, Ibrahim Gambari, da minista Fashola da takwaransa Ngige sun yi hatsari a Asaba, jihar Delta.

‘Yan sanda hudu ne ake fargabar sun mutu a hatsarin wanda aka ce ya faru ne da yammacin ranar Talata, 8 ga watan Maris.

Rahotanni sun ce manyan jami’an gwamnatin sun je babban birnin jihar Delta ne domin duba wata gada da aka gina.

Asaba, jihar Delta – Ayarin shugaban ma’aikata, Ibrahim Gambari; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da takwaransa na ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, Christ Ngige, sun yi hatsari a yammacin ranar Talata, 8 ga watan Maris.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a yayin duba wata gada a garin Asaba na jihar Delta, inda rahoton ya kara da cewa ‘yan sanda hudu ne ake fargabar sun mutu.

An tattaro cewa direban motar ne ya rude yayin tuka motar da ke dauke da jami’an tsaro inda ta fada cikin wani rami mai zurfi.

Shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya faru

Wani shaidan gani da ido, John Okorie, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da wadanda lamarin ya rutsa dasu ke tattaunawa kan kwanar da ta kai ga wajen aikin gina gadar Neja ta biyu a Asaba.

An tattaro cewa motar ‘yan sandan ta yi gudu ne don haduwa da sauran tawagar motocin ministocin ne a lokacin da ta kauce daga titi kuma ta yi hatsari.

Har ila yau, wani direba a Delta, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce:

“Lamarin ya yi muni matuka.

“Direba dan sandan yana gudu yayin da ake tattaunawa kan lankwasar hanyar wanda saboda gudun ya kasa sarrafa motar. Suka fada cikin wani rami mai zurfi. Ni ina bin bayan ayarin, ina tuki na a hankali.

“Da taimakon wasu mutane mun ceto hudu daga cikinsu amma sun samu munanan raunuka. Suna ta ihu yayin da motar ta fado musu.”

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar hatsarin ba.

Karin bayani nan tafe…

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 8 minutes 18 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 49 minutes 43 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here