Home SIYASA Sunayen Sabbin Kwamishinonin Hukumar ICPC 5 da Majalissar Dattawa ta Tabbatar da...

Sunayen Sabbin Kwamishinonin Hukumar ICPC 5 da Majalissar Dattawa ta Tabbatar da su

Sunayen Sabbin Kwamishinonin Hukumar ICPC 5 da Majalissar Dattawa ta Tabbatar da su

 

Majalisar dattawa ta tabbatar da sabbin kwamishinonin hukumar ICPC biyar bayan shugaban kasa Buhari ya zabe su.

Majalisar ta tabbatar da kwamishinonin ne a zamanta na yau Laraba, 9 ga watan Maris.

Hakan ya biyo bayan samun rahoton kwamitin majalisar wanda ya tantancesu karkashin jagorancin Sanata Suleiman Abdu Kwari.

Abuja – Majalisar dattawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Majalisar ta tabbatar da su ne a ranar Laraba, 9 ga watan Maris, bayan duba rahoton kwamitin majalisar kan yaki da rashawa da laifukan da suka shafi kudi, jaridar Punch ta rahoto.

Sabbin kwamishinonin da aka tabbatar sun hada da:

1. Sanata Anthony Agbo

2. Anne Otelafu Odey

3. Alhaji Goni Ali Gujba

4. Dr. Louis Solomon Mandama

5. Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya).

Buhari ya janye suna daya sannan ya maye gurbinsa da wani

A jawabinsa, shugaban kwamitin, Sanata Suleiman Abdu Kwari, ya tuna cewa shugaba Buhari ya janye sunan daya daga cikin zababbun kwamishinonin, Misis Mojisola Yaya-Kolade sannan ya maye gurbinta da Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya), wanda kwamitin ya tantance.

Ya bayyana cewa zababbun kwamishinonin sun bayar da amsa yadda ya kamata yayin amsa tambayoyin kwamitin kan yadda za su cika aikin hukumar.

Ya kara da cewa, bayan bincikar takardunsu, kwamitin ya gamsu da cewa wadanda aka zaba suna da kwarewa, mutunci kuma za su iya sauke ayyukan da aka zabe su suyi.”

Ya kuma bayyana cewa, babu wani rahoto na tsaro ko korafe-korafe da aka yi kan wani daga cikin wadanda aka nada.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp