Hukumomi Sun ƙwace Helikwaftoci da Otel Mallakin Tsohon Ministan Harkokin Waje na Zambia

Hukumomi Sun ƙwace Helikwaftoci da Otel Mallakin Tsohon Ministan Harkokin Waje na Zambia

Hukumomi sun kama tsohon ministan harokoin waje na Zambia Joseph Malanji kan tuhumar da suke ma sa ta halarta kudin haram.

Gwamnatin kasar ta ce Mista malanji ya shiga hannu ne bayan da bincike ya bankaɗo cewa ya mallaki wani otel da ake tuhumarsa da mallakarsa da kudaɗen al’ummar ƙasar.

Ana kuma tuhumarsa da sayen wani helikwafta kan dalar Amurka 700,000, kudaden da hukumomi suka ce na sata ne.

A baya, Mista Malanji ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.

Sai dai ‘yan sanda sun bayar da belin Mista Malanji, kamar yadda tashar talabijin ta Diamond TV ta sanar.

Ya rike mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaba Edgar Lungu, wanda ya fadi a zaben shugabban kasar da aka yi a 2021.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 26 minutes 44 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 8 minutes 9 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here