Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta haramta Al’adar nan ta tashe a Jihar.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Litinin.
Read Also:
“Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin kwamishinan ta CP Sama’ila Sha’aibu Dikko na sanar da al’ummar Jihar Kano cewa, a dakata da gudanar da Al’adar nan ta tashe, wadda ake yin ta daga 10 ga wata Azumin Ramadana, wannan ya biyo bayan fakewa da wasu bat a garin matasa ke yi da tashen suna fadan daba, kwacen waya da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi”.
SP Kiyawa ya yi kira ga iyaye da su tabbatar basu bar ‘Ya’yansu sun karya doka ba, domin kuwa duk wanda aka kama ya karya doka, ba shakka doka zatayi aiki akan shi.
Bisa al’ada, idan azumin watan Ramadan yakai kwanaki 10, akwai al’adar Tashe da kuma kidan gwauro da ake gudanarwa a kasar Hausa, wanda a wannan shekarar hukumar yan sanda ta jihar Kano, tace babu bukatar hakan, kuma tayi gargadi mai zafi ga duk wanda ya fito ya aiwatar da hakan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 46 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 27 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com