TSARO: Dakarun Sojin Hadin Gwuiwa na MNJTF Sun Hallaka Mayakan Kungiyar ISWAP.

Gamayyar Dakarun Sojin hadin gwuiwa sun sami nasarar halaka mayakan Kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP a garuruwan Malam Fatori, Damasak da Wulgo dake Yankin Kogin Chadi.

Dakarun Sojin Nijeriya Nijar da Kamuru sun fatattaki mayakan kungiyar ta ISWAP ne a mabambamta hare–haren da suka kai maboyar su.

PRNigeria ta rawaito cewa baya ga farmakin da sojin kasa ke kaiwa, an tura jiragen yaki na kai hari ta sama domin kakkabe ‘Yan Ta’addan tare da tarwatsa maboyarsu da manayan makamai.

Yayin farmakin Dakarun hadin Gwuiwar sun sami nasarar bankado manyan makamai da tarin Alburusai a hannun ‘Yan ta’addan.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com