Dakarun Rundunar Sojin Hadin Gwuiwa MNJTF sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP, Abu Fatima da wasu Karin Mayakan Kungiyar 15, a wani gagarunmin hari da suka kai maboyar mayakan a yankin Tafkin Chadi.
A ranar 9 ga Afrilun, 2022 jirgin yaki samfurin Super Tucano bisa sarrafawar Rundunar Sojin Sama karkashin Dakarun na MNJTF da kuma dakarun Mi35 hadi da dakarun Mi171 sukayi barin wuta kan dabar mayakan na ISWAP dake a arewacin Jubularam a Karamar Hukumar Marte dake jihar Borno.
Wani jami’in liken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa an kai harin ne ta sama bayan wasu bayanan sirri da aka samu kan cewa kwamandan na ISWAP na Shirin yin fito na fito da Dakarun Sojin, nan rundunar sojin ta dauki matakin kai harin.
Kwamandan Mayakan na ISWAP Abu-Fatima na da mayaka 500 a karkashin sa, kuma shike lura da yankunan Kirta Wulgo, Sabon Tumbu, Kwaleram, Sigir da Jibularam, Abbaganaram da Yarwa Kura.
Read Also:
Majiyar ta shaida cewa kwamandan ya jagoranci mabanbanta hare haren da aka kaiwa dakarun sojin Najeriya a garuwan da dama ciki har da Kukawa, Abadam, Malam Fatori duk a karamar hukumar Marte.
Zafafa hare-haren da dakarun sojin ke yi ta sama wanda COIN ke jagoranta, ya sanya mayakan na Boko Haram tsagin ISWAP neman mafaka a yankin riversbanks dake tsakanin Nijeria da jamhuriyar Niger.
Sabbin mabuyar ‘Yan kungiyar ta ISWAP sun hadar da Lumburam, Fiyoo, Lada da Jarwaram, dukkan su a yankin na riverbanks.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa a ranar 11 ga Afrilu an shigo da wasu makamai da suka hadar manyan bindigun Atilare cikin garin Tudun Wulgo da mashigar Bakkassi dake kasar Kamaru.
A yayin wata huduba salar juma da guda cikin kwamandojin kungiyar ta ISWAP ya gabatar a Sabon Tumbu, bukaci mayakan kungiyar su sake jajircewa wajen kare Daular daga farmakin soji.
Dakarun sojin hadin gwuiwar karkashin Operation lake and Desert sanity, na cigaba da kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’addar da suka hadar da cikin surkukin daji kan Tsaunuka, ruwa da dukkan maboyan ‘yan ta’addar da suka addabi yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 11 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 53 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com