Dakarun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo dauke da Makamai, sun kutsa shalkwatar hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) inda suka lakadawa kwamandan hukumar Micheal Ogar dukan kawo wuka.
Rahotan da PrNigeria ta samu ya nuna cewa tuni jami’an ‘Yan Sandan suka halaka mai tsaron lafiyar Kwamandan, bayan da Dakarun Hukumar ta Civil Defence ke kwance cikin muggana raunika.
PRNigeria ta rawaito cewa jami’an ‘Yan Sandan Kwantar da tarzo ta Mobile Police na Squadron – 18 a Jihar ta Imo ne suka aika ta wannan danyen hukunci.
Read Also:
Lamarin dai ya faru ne bayan da kwamandan ya shiga tsakanin wata takaddama daga auku tsakanin jami’in hukumar da wasu jami’an ‘Yan sanda.
Wata sahihiyar majiya ta shaidawa PRNigeria cewa lamarin ya faru tsakanin jami’an inda aka dingi musayar wuta da manyan bindigu a shalkwatar hukumar ta NSCDC dake kusa works layout a Owerri, Babban Birnin Jihar.
Binciken da PrNigeria ta gudanar ya nuna cewa rikicin ya samu asali ne bayan takaddama mai zafi tsakanin direban kwamandan Hukumar ta NSCDC na Jihar ta Imo da wani Dan Sanda a kayan gida wanda ya rufe hanyar da kwamandan zai wuce.
Har zuwan lokacin hada wannan rahoto, PRNigeria bata sami nasarar jin ta bakin Kakakin hukumomin guda biyu ba
By PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 18 minutes 26 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 59 minutes 51 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com