Home Labarai GIDAUNIYAR QATAR DA TALLAFAWAR GIDAUNIYAR MALAM INUWA TA RABAWA MARAYU KAYAN SALLAH...

GIDAUNIYAR QATAR DA TALLAFAWAR GIDAUNIYAR MALAM INUWA TA RABAWA MARAYU KAYAN SALLAH A JIHAR JIGAWA

Gidauniyar ayyukan jinƙai da taimakon al’umma ta ƙasar Qatar ta gudanar da rabon tallafin kayan sallah ɗinkakku ga yara marayu mata da maza sama da mutum (100) a Jihar Jigawa bisa tallafawar gidauniyar ba da agaji, taimako, jinƙai da ayyukan alkhairi ta Malam Inuwa, wacce mai girma shugaban hukumar (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) ya kafa.

Taron rabon kayan wanda aka gudanar a ɗakin taro na makarantar koyon aikin jinya da ungurzoma da ke Haɗejia , ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin jagoran tawagar gidauniyar ta ƙasar Qatar, Shaik Hamdi da shugabannin gidauniyar Malam Inuwa, ƙarƙashin jagorancin Dakta Hussaini Baban.

Da yake jawabi yayin rabon kayan sallar, jagoran tawagar gidauniyar ta Ƙasar Qatar, Sheik Hamdi ya yabawa gidauniyar Malam Inuwa da fadar Mai Martaba Sarkin Haɗejia a bisa haɗin kai da ƙarfafa gwiwar da su ke ba su a duk lokacin da su ka nufaci gudanar da ire-iren waɗannan ayyukan alheri.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban gidauniyar ta Malam Inuwa, Dakta Usaini Yusuf Baban ya bayyana godiya da addu’ar fatan alkhairi ga gidauniyar bisa wannan ayyuka da su ke yi, inda ya jadda aniyarsu ta cigaba da marawa ayyukan gidauniyar baya duba da yadda ita ma gidauniyar ta ke ƙoƙari kan wannan aiki inda ko da a wannan wata na Ramadan ta yi rabon tallafin shinkafa ga marayu ɗari-ɗari a kowacce ƙaramar hukuma tare da raba kayan sallah ga marayu da dama.

Taron ya samu halartar sakataren kwamitin marayu na Jihar Jigawa Shaik Abdulƙadir Zakar, da na’ibin limamin masarautar Haɗejia, Malam Umar Hamza Abbas da sauran masu ruwa da tsaki.

Yara marayun da su ka amfana da wannan tallafi sun bayyana farin cikinsu matuƙa da godiya bisa wannan abin alkhairi da aka yi musu gami da addu’ar Allah Ya ba da lada.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp