CIN HANCI: EFCC Ta Kwace Jami’a, Masana’anta, Otal Mallakin Daraktan Kudi

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Nijeriya  ta EFCC ta kwace Jami’a, Masana’anta, Otal dake da alaka da daraktan kudi.

Wannan na kunshe ta cikin wata takardar sanarwa da aka raba ga manema labarai mai dauke da sa hannun kakakin hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren, mai kwanan watan 1 ga watan Yunin 2022.

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a Birnin tarayyar kasar Abuja, a yayin zaman shari’ar daya gudana ranar laraba 1 ga watan Yuni 2022, ta bada Umarnin karbe dukkan wata kadara dake da alaka da jami’ar NOK,  wadda ke jihar Kaduna.

Jami’ar wadda tsohon daraktan Kudi na DFA a ma’aikatar lafiya ta tarayya Anthony Hassan ya gina, ana zargin an gina ta ne daga kudaden haramun da aka bi diddigin mamallakin jami’ar.

Hassan ya rike mukabin Daraktan Kudin na DFA a ma’aikatar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, ana zargin ya gina jami’ar ne da kudin haramun, yanzu dai haka akwai gine-ginen da suka hadar ginin majalisar zartarwar jami’ar, ginin shahen ICT, Sashen Nazari da kirkirar Magunguna, sashen kimiyya, gine-gine shashen manyan Malamai Ajujuwan karatu da suran gine-gine.

Sauraran kadarorin da aka gani mallakin Hassan, wadanda kuma aka kwace su na wucin gadi sun hadar da Gwasmyen water factory, Gwasmyen Event Center da Gwasmyen International Hotel dake jihar kaduna.

Mai shari’a Zainab Abubakar, ta bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi yayin da take yanke hukunci kan karar da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta shigar gabanta.

Lauyan hukumar ta EFCC Ekele Iheanacho ya shaidawa kotun cewa hukumar na neman wannan umarni ne dogaro da sashi na 44 (2) na kudin tsarin mulkin nijeriya na shekara 1999 (wanda aka yiwa gyaran fuska) da kuma sashe na 17 na kudin yaki da Zamba, laifukan da suka dangaci doka mail amba ta 14, 2006 da kuma karkashin ikon kotun mai girma.

PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 31 minutes 54 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 13 minutes 19 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com