Home Labarai Dakarun Sojin Sama Sun Halaka Mayakan ISWAP 13 Tare da Kama 5

Dakarun Sojin Sama Sun Halaka Mayakan ISWAP 13 Tare da Kama 5

Dakarun sojin saman Nijeriya sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar Boko Haram tsagin ISWAP, a yakin Arewa Maso Gabashin kasar kamar yadda PRNigeria ta rawaito.

Mayakan da dakarun suka halaka da sanyin safiyar Litinin sun sanya shingen tsare ababa hawa a hanyar  Goni Masari dake kusa da hanayar Maiduguri zuwa Damaturu, a jihar Borno.

Dakarun rundunar sojin  sun sami wani rahoton sirri daya bayyana yadda mayakan suka tare kan hanyar wanda tuni har sun sami damar yin garkuwa da wani matukin mota, nan basuyi kasa a gwuiwa ba suka farmake su da jiragen yaki.

A cewar kwmandan daya jagoranci kai harin yace dakarun sojin sun sami nasarar kubutar da wanda akayi garkuwa dasu su 5, a harin da suka kai wa ‘yan ta’addan.

Kwamandan, wanda ya ki bayyana sunansa ga PRNigeria, yace sojojin sun halaka mayakan kungiyar ta ISWAP sama da 13, tare da raunata wasu da dama, inda suka sami nasarar kwato motar dake dauke da bindiga da suka bari a wajen.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp