Gabanin Babban zaben shekarar 2023, shalkwatar tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bukaci ‘yan siyasar kasar da su bi hanyaar data dace wajen cika muradin su.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan, yayin da yake wata ganawar mako-mako da manema labarai a birnin tarayyar Abuja.
Yace wajibi ne ‘yan siyasar su bar kasar ta zauna lafiya, ta hanyar gujewa ayyuka da maganganun da ka iya kawo cikas ga tsaron kasar yayin yakin neman zabe.
Read Also:
A cewar Irabor, “Nijeriya kasar mu ce, yanzu hakan mun shiga kakar zabe kuma kowa na bukara a gudanar da zaben da yakin neman zaben cikin lumana, naji dadin yadda shugaban kasa ya shaidawa Al’ummar kasar abinda yake so amma kar a yi tunanin cewa hakkn gwamnati ne ita kai ta tabbatar anyi zaben cikin kwanciyar hankali.
“Abu mafi Muhimmanci dangene da zaben da ke tafe, shi ne mu kasance mazan mu da mata mun ggudanar da shi cikin kwnciyar hankali, kuma ina bukatar ku tura wannan sako zuwa ga kowa da kowa, dukkan wanda yake son yin zabe yayi shi cikin doka da odar, domin kuwa zamu tsaya a gefe muga masu tada tarzoma, domin neman mukamai.
Daga bisani ya bayyana cewa Nijeriya kas ace wacce dole ne a azauna lafiya don haka kada mu bari masu aikata laifi ko ‘yan daba su yi amfani damu wajen wargazata, don haka muna goyon bayan jami’an ‘yan sanda don basu duk wani talafi domin cigaban Nijeriya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 32 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 14 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com