Home Labarai Hadirin Mota Yayi Sandiyyar Mutuwar Mutum 7 Tare da Jikkata 5

Hadirin Mota Yayi Sandiyyar Mutuwar Mutum 7 Tare da Jikkata 5

Hukumar kiyaye Aukuwar hadurra reshen jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutum 7 kuma mutum 5 sun jikkata, yayin da wasu motoci 2 sukayi taho mu gama a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja a ranar Alhamis.

Kwamandan shiyya na na hukumar ta FRSC, Stephen Dawulung ne ya tabbatar aukuwar lamarin ga manema labarai a garin lokoja ranar Juma’a.

Yace lamarin ya faru ne yayi da wata mota Bus kirar Toyota Hiece tayi gaba da gaba da wata mota kirar Daf a garin Akpanya dake daura da koton karfe a hanyar Abuja zuawa lokoja.

“yayin da motocin 2 sukay taho mu gama, mutum 7 suka mutu nan take, inda mutum 5 kuma suka sami raunika a sassan jikin su.

“Jami’an mu sun garzawa wajen da lamarin ya faru bayan samun rahoto, nan suka shiga ikin taimako nan kuwa suka taimaki musamman wadanda suka ji rauni da taimakon gaggawa.

“tuni dai an garzaya da wadanda suka ji raunin zuwa asibitin koton karfe, inda ake lura da lafiyar tasu, an kuma an ajje wadanda suka mutu a warin ajiyar gawarwaki na asibiti (Mortuary) kamar yadda ya bayyana.

Dawulung ya bayyana cewa hadarin ya auku ne sakamakon Gudun wuce sa’a da matuka Ababan hawan ke yi a yayin da suke tsaka da tuki.

Daga bisani ya bukaci Al’umma, musamman matuka Ababan hawa da su gujewa tafiyar dare, tare da yin gudun wuce sa’a, yayin tukun kuma su tabbatar sun bi dokoki da ka’idojin hanya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp