‘Yan Sanda Sun Halaka ‘Yan Ta’adda Tare Da Kama Wadda Ke Musu Safarar Makamai A Kaduna

Dakarun rundunar yan sandan Nijeriya ta musamman dake birnin tarayya Abuja hadin gwuiwa da Dakarun Operation Yaki sun sami nasarar halaka ‘yan Ta’adda guda 4 tare da kame wata mata dake musu safarar Alburusai akan babbar hanyar Saminaka zuwa Jos a Jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka rana ga manema labarai, sanarwar tace lamarin ya auku ne ranar laraba 15 ga watan Yuni, yayi da ‘yan sandan suka kama ‘yan bindigar cikin wata shudiyar mota (blue) wadda James Dawi mai kimanin shekaru 31 dan asalin garin Vom na karamar hukumar Jos ta kudu a Jihar Plateau.

Sanarwa ta kara da cewa maharani sun gamu da gamon su a hanayar su ta kai wasu muggana makamai ga tawagarsu, inda suka yi musayar wuta da jami’an.

“kwararrun Jami’an sun sami nasarar raunata wasu mutane 4 da ake zargi. Yayin da aka garzaya da su asibitin koyarawa na Barau Dikko dake Kaduna, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su, said ai ya tabbatar da cewa wasu cikin ‘yan bindiga sun tsere daji da raunukan harbi a cikin su.

Ya kara da cewa yayin da dakarun ke gudanar da bincike a cikin motar, an gano bindiga kirar AK49 guda 1dauke da alburusai guda 6, tare da wani kwanson masakin alburushin, da kuma wasu tarin Alburusai guda 134 da kuma wata mota guda 1.

Yace dakarun a yayin atisayen sun kuma kama wata mata, wadda da ake gudanar da bincike ta amsa cewa ita ke yiwa ‘yan bindigar safarar makamai a jihar Kaduna.

Daga bisani ya bayyana cewa hanzu haka dai hukumar ‘yansandan jihar na zurfafa bincike kan lamarin.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 29 minutes 18 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 10 minutes 43 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com