Home Labarai ‘Yan Jarida Mata Sun Wallafa Littafi A Wani Bangare Na Bikin Zagayowar...

‘Yan Jarida Mata Sun Wallafa Littafi A Wani Bangare Na Bikin Zagayowar Haihuwar Yahaya Bello

Mawallafan Gungun rukunin Kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), PRNigeria, Economic Confidential, Politics Digest, sun kaddamar da wani littafi da wasu mata ‘yan jarida biyu suka rubuta akan Gwamnan jihar Koji Yahaya Bello a bikin cikar sa shekaru 47 da haihuwa.

Littafin mai suna “Yahaya Bello: 47 Narratives on a Change Agent,” an gabatar da  shi ga gwamnan yayin bikin cikar shekarar sa 47 da haihuwa a birnin tarayya Abuja.

Babbar wakiliya a jaridar Politics Digest Nafisat Bello da kuma wakiliyar jaridar tattalin arziki ta Economic Confidential Hafsat Ibrahim ne suka rubuta littafin mai shafuka 183, wanda ya kunshi siyakin gami da bayanin ayyukan Gwamna Yahaya Bello guda 47, wanda marubutana suka fara tattarawa tun a watan oktoban shekarar da ta gabata.

Da yake jawabi babban jami’in kamfanin na IMPR, Yusha’u A. Shuaib, yace wadannan siyakin ayyuka 47 da suka tattara yayi daidai da adadin shekarun da Gwamnan na haihuwa, inda ya kawo gagarumin cigaba a fannin tsaro, tattalin Arziki, gami da samar da ababen more rayuwa, ayyukan yi, karfafa mata da matasa da kuma yunkirinsa na neman kujera mafi girma a Nijeriya a ‘yan tsakanin nan.

Da yake bayyana jin dadin sa game da Littafin Yahaya Bello ya Godewa Alh. Shuiab bisa wannan kyautar bazata da aka yi masa a ranar zagayowar haihuwar sa tare da yin alkawarin cigaba da yin aiki tukuru don ganin an cigaba da samun cigaba mai dorewa a jihar ta Kogi.

Ya kuma nuna godiyar sa ga marubutan mata guda biyu, wadanda ‘yan asalin jihar Kogi ne, ya kuma yaba da jajircewarsu, sadaukar, tare da tabbatuwa akan wannan  gwadabe na aikin da suka dauke tun a shekarar data gabata.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp