A karkashin Mulkin Buhari, An Hallaka Sama Da Mutum 3,478, An Sace 2,256

Wani rahoton bincike a Najeriya ya ce akalla mutane dubu 3 da 478 aka kashe a Najeriya tsakanin watan Disambar bara zuwa Yunin bana, yayin da aka sace wasu dubu 2 da 256 sakamakon tabarbarewar tsaron da ya addabi kasar.

Kungiyar da ke sanya ido akan harkokin tsaro da ake kira ’Nigeria Security Tracker’ da ke samun goyan bayan wata Majalisa a Amurka ta gabatar da wadannan alkaluma masu tada hankali.

Rahotan kungiyar ya danganta kisan da kuma sace mutanen da akayi a cikin watanni 7 da suka gabata da ayyukan ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga da ‘Yan fashi da makami da ‘Yan kungiyar asiri da kuma jami’an tsaro.

Alkaluman da kungiyar ta gabatar yace a watan Disambar bara, an kashe ‘Yan Najeriya 342, yayin da aka sace wasu 397, cikin wadanda aka kashe harda manoma 45 a Jihar Nasarawa da kuma mata 34 da aka sace a Jihar Zamfara.

A watan Janairun wannan shekara, kungiyar tace akalla mutane 844 aka kashe, yayin da aka sace 603, cikin su harda mutane sama da 200 a yankunan Jihar Zamfara da 220 da aka kasha a Neja, sai kuma 200 da aka sace a Jihar.

A watan Fabarairu kuma, kungiyar tace mutane 495, bayan sace 326, cikin su harda 33 wadanda suka ki biyan harajin naira miliyan 40 da yan bindiga suka sanya musu a Jihar Zamfara, sai kuma 44 da aka kashe a Jihar Neja, tare da sace 31.

Sakamakon binciken yace a watan Maris, mutane 606 akayi asarar rayukan su, tare da sace wasu 450 cikin su harda Yan Sakai 63 a Jihar Kebbi da kuma mutane 26 da aka kashe a harin da ake danganta shi da ramako a Jihar Taraba.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 52 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 34 minutes 21 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com