Rundunar Sojin Nigeria Ta Yabawa Jaridar PRNigeria

Rundunar Sojin Nigeria ta yada da yadda jaridar PRNigeria ke gudanar da ayyukan ta tare da bada Gudunmawa wajen tabbatuwar tsaro a kasar

Daraktan yada labaran Rundunar sojin Nijeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan yayi da yake jagorantar tawagar jami’an runduna wajen miki ta’aziyya ga babban Editan jaridar PRNigeria da Economic Confidential Yusha’u Shuaib bisa rasuwar mahaifin sa Imam Abdulhameed Agaka.

A ziyarar ta’aziyya ta kafa da kafa bisa wakilcin Daraktan yada labaran ta rundunar ta bayyan rashin Imam Agaka matsayin Babban rashi ga Al’ummar Nijeriya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali baba, ya mika tashi ta’aziyya ta cikin wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi, inda yace sufeto janar din yayi Addu’ar samun rahama ga Imam.

Fitaccen malamin addinin musulunci, kuma babban Limamin Al’ummar garin Agaka dake karkashin masarautar ilori a jihar kwara, ya rasu a wani asibiti mai zaman kansa, bayana wata gajeruwar rashin lafiya, a farkon watan Yuni yana da shekara 77 a duniya.

Nwachukwu, ta cikin ta’aziyyar daya jagoranci tawagar hafsoshin soji suka kai wa Shuib a babban Ofishin jaridar ta PRNigeria dake Birnin tarayya Abuja, ya bayyana kaduwa matuka bisa samun labarin rasuwar shaiek Abdulhameed Agaka.

Ya bayyana rasuwar Imam Agaka matsayin tashin hankali, wanda tabbas ya sanya Al’ummar garin Agaka har ma da iyalan sa jin radadi gami da shiga cikin rudani.

Sai dai ya tabbatar da cewa Shiek Agaka yayi rayuwa mai cike da al’barka wadda ake kyautata zaton samun rahamar Allah a gare shi.

Janal Nwachukwu yayin mika ta’aziyyar yace babban hafsan sojin Nijeriya COAS, laftanar Janar Faruq Yahaya, yay aba da dokarin da jaridar PRNigeria ke yin a fito da martabar Rundunar Sojin Nijeriya da dakarunta baki daya.

“Mun yaba da dukkan abinda PRNigeria k uke yi wa sojojin Nijeriya, sannan kuma sojoji suna kallon ku a matsayin abokan hulda, wajen hadin gwuiwa domin kawo cigaba. Kamar yadda ya fada.

Ta cikin wata wasikar ta’aziyya mai dauke da sa hannun CSP Adejobi, Sifeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya IGP Alkali Baba, ya mika ta’aziyyar sa a madadin rundunar ‘yan sandan Nijeriya baki daya.

Ya kuma yi addu’a samun rahamar Allah ga Sheik Agaka, tare da fatan Allah ya sanya Aljanna ce makomar sa.

“Ya rasu daidai lokacin da kasarnan ke bukatar sa a matsayin babban malami dake yada Addinin Musulunci yadda ya aka aiko Ma’aikin Allah dashi, ya kuma taka muhimmiyar rawa fanin sanya Al’ummar a tafarkin yin hakuri da juna a tsakinan Al’ummar da yayi rayuwa dasu. Inji IGP

By PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 51 minutes 10 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 32 minutes 35 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com