‘Yan Bindiga Sunyi garkuwa Da DPO A Jihar Kaduna

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kama sabon baturen ‘yan sanda da aka tura karamar hukumar birnin Gwari dake jihar kaduna.

Anyi garkuwa da baturen ‘yan sandan ne akan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safiyar ranar litinin a yayin da yake kokarin zuwa inda aka turashi domin kama aiki.

Wata majiya ta sai dawa PRNigeria cewa baturen ‘yan Sandan (DPO) na kan hanyar sa zuwa birnin Gwari masu garkuwar suka kama shi, sai kawo yanzu ba’a tabbatar da ko yayi tafiya shi kadai bane ko akasin haka.

Kawo yanzu dai hukumar ‘yan sandan jihar na tattara bayanai domin fidda sanarwa a hukumance, kamar yadda kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna Muhammad Jalige ya bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com