Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da kudirin ta na bada fifiko wajen magance rikice-rikice da kuma dakile cutar da fararen hula a yayin da jami’an ke kokarin kawar da masu data kayar baya.
Kwamandan Kwalejin tsaro ta kasar Rear Admiral Murtala Bashir ne ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani da cibiyar yaki da rikece-rikice (CIVIC) tare da hadin gwuiwar tsofaffen daliban kwalejin tsaron ta kasa (AANDEC) suka shirya a wani bangare na magance cin zarafi da ake zargin jami’an na yiwa fararen hula.
Da yake jawabi daraktan cibiyar ta CIVIC ta kasar Mr Benson Olugbuo ya jaddada cewa kare fararen hula a yanayin tsaro na da matukar muhimmanci saboda yawaitar rikice-rikicen a fadin kasar.
Read Also:
Ya bukaci dakarun tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin Al’umma, tare da yin dukkan mai yiwuwa wajen dakile cutar da fararen hula a yayin gudanr da ayyukan wanzan da zaman lafiya.
Olugbuo ya bayyana cewa na daga cikin dalilin daya sa aka gudanar da taron, domin atabbatar da cewa sojoji sun bi ka’idojin aiki a yayin gudanar da ayyukan tsaro.
Shima da yake bayani a yayin bitar Shugaban Tsofaffin daliban kwalejin na kasar Air Commodore Darlington Abdullahi (Mai ritaya) ya bukaci fararen hula da su hada kai da sojoji ta hanayar musayar sahihan bayanai da zai taimaka wajen yakar ‘yan ta’adda masu tada kayar baya.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 51 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 32 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com