Home Labarai Dakarun Sojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Kubutar Da Mutum 6 Tare da...

Dakarun Sojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Kubutar Da Mutum 6 Tare da Hallaka ‘Yan Bindiga a Jihohin Zamfara Da Katsina

Dakarun sojin Nijeriya karkashin rundunar hadarin Daji sun sami nasarar kubutar da wadanda ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su a Rafin Bakura dake karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Wannan dai na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar Sojin kasar Manjo Janar Benard Onyeuko, sanarwa mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Yuni 2022 tace bayan wani kiran gaggawa da suka samu kan ayyukan ‘yan ta’addan a Rafin Dankura, dakarun su suka tasamma ‘yan bindigar dake shirin yin garkuwa da mutanen nan ne suka sami nasarar kubutar da mutum 6 tare da hallaka ‘yan bindigar guda 2.

Oyeuko yace a yayi sumamen dakarun sun sami nasarar kwato bindiga kirar AK47 guda biyu, gurneti hadin gida guda 2, wayoyin hannu guda 2 da kuma zunzurutun kudi kimanin naira Dubu Biyu da Casa’in da Tara (299,000).

Dakarun sojin saman na Operation HADARIN DAJI  a wani farmaki da suka kai ta sama a ranar 22 ga watan yuni, a kauyen kofar Danya dakare karamar hukumar  Bukkuyum ta jihar Zamfara, bayan wani rahoton hari da aka shirya kaiwa kauyen, rundunar ta sami damar zuwa wurin, inda ta hangi ‘yan ta’addan da sama wanda sun haura dari da hamsin (150) a wata maboyar su.

Nan dakarun suka shiga yin artabu da ‘yan ta’addan wanda hakan yayi sanadiyyar tarwatsa sansanin na su, sakamakon hakan sahihan bayanan dake fitowa daga mazauna yankin na kofar Danya sun ce sama da ‘yan bindiga 82 sun sami muggan raunuka inda aka kashe da dama daga cikin su.

Haka a wani harin makamancin wannan da dakarun su kai kauyen mai gra dake karamar hukumar Faskari a jihar katsina, sun sami nasarar halaka ‘yan ta’addan guda biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp