An bukaci Jami’an yada labaran (PROs) na Hukumar (NCS) Da Suke Yin Amfani da Kayan Aikin Yada Labarai Na Zamani

An bukaci Jami’an yada labaran (PROs) na hukumar hana fasa kwauri na Nijeriya (NCS) da suke yin amfani da kayan aikin yada labarai na zamani.

An yi wannan kira ne a yayin wani taron horaswa da hukumar ta shirya wa masu Magana da yawunta.

Da yake Magana a wajen taron horaswa kwamandan dake lora da sashen horas da jami’an Kwastam (CTC) dake Ikeja, Kwantorola Kalamu Ayinde Aremu, ya bayyana cewa yin amfani da sabuwar fasahar zamani zai taimaka matuka wajen sake daga darajar hukumar.

Kakakin hukaumar na kasa DC Timi Bomodi yace, an gadanar da wannan horaswa domin  baiwa jami’an sashin hulda da jama’a na hukumar horon da zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukan su yadda ya dace da zamani.

Da yake gabatar da Makala mai take “Effective Public Communication” a yayin taron horaswar Babban mai tace Labarai na jaridar PRNigeria, Yushau Shuaib ya bayyana cewa an sami gagarumin cigaba a fannin sadarwa, ta hanyar sauyi aka samu wajen yin hulda da jama’a.

Sauran wadanda suka gabatar da Makaloli kan matsalaolin da jami’an ke fuskanta, a yayin taron horaswar sun hadar da Dr. Ganiu Okunnu na Jami’ar jihar Legas (LASU) da Abayomi Adisa na BBC, sun bukaci mahalarta taron dasu yi amfani da kayan sadarwa na zamani a yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Wanda suka ce yin hakan zai taimaka musu matuka wajen samun kyakkyawar alaka da wadanda suke son sakon ya isa gare su.

By PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 50 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 31 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com