Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ICPC ta gurfanar da mataimakin kwamandan hukumar dake bada kariya ga fararen hula ta Civil Defence Mr Boutidem Akpan gaban kotu kan zarginsa da badakalar kudaden da suka kai naira miliyan 26 da dubu dari 655.
An gurfanar da Mr Akpan gaban mai shari’a V. S. Gaba na babbar kotun tarayya dake Kwali a birnin Abuja ne bisa tuhumarsa da laifuffuka 17 dake da jibi da almundahana da dukiyar kasa, da ya hadar da amfani da sunan kamfaninsa wajen damfara.
Cikin takardar tuhumar dai ta nuna ana zarginsa da amfani da kujerarsa wajen yaudarar wasu mutane ta hanyar karbar kudi daga hannunsu da sunan hukumar, yana mai cewa hukumar ce za ta raba musu filaye a yankin Karshi da Sabon Lugbe da kan titin Filin jirgi da kuma wasu filaye a jihar Nassarawa, wanda kuma kawo yanzu ba a bas u filayen ba.
Hukuar ICPC dai ta shaidawa kotu cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 kuma laifukan sun saba da sashi na 19 da 26 karamin sashi na 1 sakin layi na 3 na kundin dokokin hukumar na shekarar 2000.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 19 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com