Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta Nemi afuwar Maniyatan kasar na bana dangane da wahalhalun da suka Sha yayin jigilar maniyatan daga kasar zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar aikin Hajjin bana.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’ar yada labaran hukumar NAHCON Fatima Sanda Usara ta fitar tace Hukumar ta kuma Nemi afuwar gwamnatin tarayyar kasar, da hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, masu kamfanonin jirgin yawo, sauran jama’a kan duk abubuwa marasa dadi da suka faru a makonnin da suka gabata.
Abin takaicin shi ne, duk da kokarin da aka yi na jigilar dukkan maniyyatan Najeriya da ke da niyyar zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2022, NAHCON ta gaza wajen sauke wannan nauyi, musamman dalilin koma bayan da aka samu a karshen makon da ya gabata, wanda ya kawo cikas ga shirinta na kammala jigilar maniyyatan zuwa ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara.
Read Also:
“Sai dai abin takaicin shi ne, yadda kamfanonin jirgin da muka zaba kuma suka bamu tabbacin zasu iya wannan aikin Amma su ne silar duk wadannan matsaloli da muka samu na kasa kammala jigilar dukkanin maniyatan kasar nan zuwa kasa mai tsarki.
Musamman, wadannan adadin maniyyatan da abin ya shafa ba sune muka gaza kaisu kasar saudiyya har lokacin rufe filin jirgi sama na jidda ,wanda hakan ya tabbatar da cewa sun rasa aikin Hajjin na bana. akwai maniyatan tara (9) daga jihar Bauchi; maniyatan 91 daga jihar Filato; Maniyata 700 ne daga jihar Kano da kuma mahajjata kimanin 750 daga bangaren masu bin jirgin yawo.
Sanarwar tace Hukumar ta ba da tabbacin cewa za a mayar wa dukkan maniyyatan da abin ya shafa kudin aikin Hajjinsu yayin da za ta yi kokarin gyara matsalolin da a nan gaba.
NAHCON ta koyi darussa da dama kuma ta kuduri aniyar ganin hakan bata a sake faruwa ba, Hukumar bata da kalmomin da zata yi amfani dasu wajen hakurkurtar da yan Nigeria musamman wadanda suka kudiri aniyar aikin Hajjin sakamakon mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 52 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 33 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com