Home Labarai Bincike: Shin Da Gaske Ne Kashim Shattima Yayi Karin Kumallo Da Mayaka...

Bincike: Shin Da Gaske Ne Kashim Shattima Yayi Karin Kumallo Da Mayaka Masu ikirarin Jihadi A Jihar Borno?

KORAFI: Wasu hotuna da suka dauki hankulan al’umma da  aka yada a kafafen sada zumunta na Facebook da whatsapp  sun nuna yadda Dan takarar Mataimakin shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC Senator Kashim Shettima, yake Karin kumallo da ‘yan bindiga.

CIKAKKEN BAYANI: wasu hotuna sun yadu a kafafen sada zumunta, wanda suke nuna yadda sanator Kashim Shatima, kma tsohon gwamnan jihar Borno, wadanda ke nuna yadda ya dauki hoto da wasu da ake zargin mayaka masu tada kayar baya ne, wanda aka nuna sun a cin tsire da biredi da kuma Ruwan roba.

Hoton da aka yi masa take “yan bindiga na Karin kumallo da Mai gidan su. Chanki waye? Mataimakin Tinubu, Kashim Shettima.”

An sami zazzafan ce-ce-kuce tsakanin mabiya addinin Kirsita da Musulmi tun bayan da aka sanar da Musulmi a matsayin wanda zai yiwa Dan takarar shugabancin kasar karkashin inuwa jam’iyyar APC mataimaki. Wasu daga cikin mabiya addinin kirsitanci a kasar sunyi ikirarin cewa  ba adalci bane dan takarar shugaban kas ana Jam’iyyar APC ya zabi wanda zai tsaya takarar dashi daga cikin mabiya addinin Musulunci kasancewar addinin su daya duba da yadda kasar take

RA’AYIN MAI BINCIKE: tun bayan ayyana sanata Kashim Shettima matsayin mataimaki ga dan takarar shugaban kas ana jam’iyyar APC Asiwajo Ahmad Tinubu, wasu cikin Al’ummomi suka fara nuna cewa an yi son kai a zabin nasa, gami da kalubalantar hadin.

Guda cikin irin wadannan kalaman kalubalanta kuwa, an dingi yada wasu hotona na sanata shettima tare da wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne ko kuma ‘yan Ta’adda.

Fact-check: Is it true that between 2010- 2018, Ekiti State Ran on a Christian – Christian ticket?  – PRNigeria News

BINCIKEN TABBATARWA:

Ta cikin wani cikakken faifen Bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu Sanata kashim Shettima yana cin abinci tare da Fulani makiyay a yankisu, lokacin da ya kai musu wata ziyarar lallashi a kokarinsa na shawo kan su, su sanya ‘ya’yan su makaranat domin su ci gajiya tsarin nan na Ilimi kyauta a wannan yanki, wannan faifen bidiyon ke nuna Zahiri sanata Kashim ne.

A kuma wannan ziyara ne shatima ya sami damar cin abinci tare da wadancan shuwagabannin Fulani.

Wannan kuma na cikin wani faifen bidiya mai dauke da kwanan watan Oktoban 2017, da kashim ya wallafa a shafin s ana sada zumunta.

Faifen bidiyan kuwa yayi masa taken “Muna Shigar da yaran Fulani makiyaya Makaranta a karkashin shirn bayar da tallafin Karatu kyauta.

“ A karkashin wannan Shirin, muna jan hankalin iyaye da yara tare da Dimbin Al’ummar dake wannan yanki don yin rijiistar shiga wannan tsari.

Idan za’a iya tunawa, a watan Oktoban 2017 ne Gwamnan Jihar Borno na wancan lokaci, kashim Shettima ya kaddamar da Shirin baiwa ‘ya’yan Fulani Makiyaya rijistar a makarantu kyauta, tare da jan hankalin Fulanin don ganin an dakile yawan fadace-fadace dake haifar da rashin zaman lafiya a cikin Al’umma.

Haka kuma ko da a watan Disambar 2018, Uwar Gidan Shugaban kasa Muhammad Buhari Aishata kaddamar da bude makaranta wadda aka sanaya mata suna “Aisha Buhari Integrated School for Nomadic community” a garin Maduguri.

Makarantar wacce Gwamnatin Borno karkashin jagorancin Kashim Shettima ta samar da ingantattun kayan aiki, gani da inganatccen yanayi domin koyo da koyarwa.

Shettima ya gana da iyayen yaran da dama, haka kuma an dauki lokaci ana wayar da kai tare da karawa Fulani makiyaya kwarin gwuiwa, abinda ya sanya Fulanin bada yaransu da dama domin saka su a makarantar, hakan kuma ya taimaka matuka wajen kawar da tashe tashen hankula daya ke da alaka da faulani makiyaya a jihar ta Borno.

HUKUNCI/ DAGA KARSHE

Maganar cewa Sanata Kashim Shattima ya yi Karin kumallo da ‘yan fashin, KARYA ce. Dangane da hujjojin da PRNigeria ta tatta daga Faifan Bidiyon da tayi masa kallon kurulla tare da tattara rahotannin daga wasu kafafen yada labarai, sanata Kashin Shettima bai taba cin abincin safe ( Karin kumallo) da ‘yan ta’adda ba.Don haka Da’awar ba GASKIYA ba ce.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp