Biyo bayan rahotannin da ke cewa gwamnatocin jihohin kasar na kokarin dakile ayyukan zaben jam’iyyun adawa da na ‘yan takararsu, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi Allah-wadai da irin wannan dabi’a, inda ta ce a shirye take ta hukunta jihohin da aka samu irin wannan lamari.
A cewar INEC, dukkan jam’iyyun da za su shiga zabukan 2023 suna da ‘yancin gudanar da yakin neman zabe a dukkan jihohin kasar nan 36.
hukumar ta alakatan hakada Jadawalin Ayyuka na yakin neman zaben 2023 na Jam’iyyun siyasa kamar yadda aka tanada a sashe na 94 (1) na dokar zabe ta 2022.
Read Also:
Don haka hukumar ta gargadi gwamnatocin jihohi da kada su hana sauran jam’iyyun siyasa yakin neman zabe a yankunansu.
Babban sakataren yada labarai na shugaban hukumar ta INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce akwai hukuncin da ya saba wa wadannan tanade-tanade kuma doka ba zata sassautawa mutum ba komai girman daraja.
Oyekanmi ya ce dokar ta ce za a raba lokacin iska / sararin kafofin watsa labarai na lantarki da na bugu, na jama’a ko na sirri, za a ba su daidai wa daida tsakanin jam’iyyun siyasa ko ‘yan takara a sa’o’i iri ɗaya na ranar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 33 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 14 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com