Home Labarai Kotun Daukaka Kara a Nijeriya ta yi Watsi da Tuhume-Tuhume da ake...

Kotun Daukaka Kara a Nijeriya ta yi Watsi da Tuhume-Tuhume da ake wa Nnamdi Kanu

Kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar gwamnati tarayya a kan jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.

Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.

Alkalan sun ce an dawo da shi Najeriya ne ba bisa ƙa’ida ba.

Sannan sun ce gwamnatin tarayya ta gaza faɗar wajen da ta kama Kanu duk da manya-manyan zarge-zargen da take yi masa.

Kotu ta ƙara da cewa shirun da gwamnatin ta yi na nuna cewa ta yarda da abin da Kanu ya ce na cewa sato shi aka yi aka dawo da shi Najeriya da ƙarfi.

Kotun ta ce tsare Kanu da yi masa shari’a a kowace kotu karya doka ne tun da ba bisa ƙa’ida aka mayar da shi Najeriya ba.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan Kanu kuma ɗan rajin kare hakkin ɗan adam, Ifeanyi Ejiofor, ya rubuta a shafinsa Facebook a ranar Alhamis cewa, “a ƙarshe dai Kanu ya yi nasara.

“An ba da damar ɗaukaka ƙara, an saki tare da wanke Oyendu Mazi Nnamdi Kanu. Mun yi nasara!, ya rubuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp