Wata Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yola ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, wanda Sanata A’isha Binani ta sami nasara.
A hukuncin da ta yanke, mai shari’a A.M Anka ta buƙaci Aisha Binani ta daina bayyana kanta a matsayin ƴar takarar gwamna a zaɓen gwamna na shekara ta 2023.
Kotun ta ce zaɓen ya zama haramtacce saboda aringizon ƙuri’a da kuma kawo wakilai daga ƙaramar hukumar Lamurde, inda ba a gudanar da zaɓen cikin gida na jam’iyyar ba.
Read Also:
Tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa (EFCC) Mallam Nuhu Ribadu ne ya shigar da ƙarar, inda ya buƙaci kotu ta soke zaɓen, wanda aka gudanar a watan Maris.
Inda ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u, da sayen ƙuri’a da kuma bai wa daliget cin hanci.
Yanzu haka kotun ta ce jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar gwamna a jihar ta Adamawa a zaben shekara ta 2023.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 8 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 49 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com