Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da kyautar lambar girman shugabanci na gari akan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu fitattaun ‘yan Najeriya 43.
Read Also:
Ita dai wannan lambar girma an ware ta ne ta musamman domin girmama wasu jama’ar kasar da suka bada gudumawa a matakin kasa ko jiha ko kananan hukumomi ko kuma ayyukan gwamnati ko na jinkai.
Sharuddan karbar lambar girma sun hada da bada gudumawa a matsayin ma’aikacin jama’a ko kuma fice a aikin da mutum yake yi na kansa ko nuna rayuwa ta gari a tsakanin jama’a ko yin wani aikin da jama’a zasu ci gajiyar sa.
Ana saran ma’aikaci ya nuna a bayyana yadda yake gudanar da aikin sa fiye da yadda ake bukata a tsakanin al’umma.