Rundunar sojin Nijeriya ta jaddada kudirinta na hada kai da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin samar da cikakken tsaro da kuma tabbatar da an gudanar da zaben shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali.
Babban kwamandan rundunar sojojin Najeriya ta 7, Manjo Janar. Waidi Shuaib, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma daya kaiwa kwamishinan ‘yan sanda jihar Borno, Abdu Umar, a birnin Maiduguri ranar Talata.
Read Also:
Ya ce hada kai tsakanin sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zai taimaka wajen samar da tsaro mai yawa kafin zabuka da kuma bayan babban zabe.
GOC ya ce ziyarar za ta ba shi damar yi masa fashin tunani game da shirye-shiryen ‘yan sanda don magance matsalolin tsaro a lokacin zabe.
Mista Abdu ya ce rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da hada kai da sojoji domin kare rayuka da dukiyoyi a Borno, kuma rundunar ta zafafa sintiri tare da hadin gwiwar rundunonin sojoji domin yakar munanan laifuka a cikin birnin Maiduguri.
Shugaban ‘yan sandan ya sake nanata shirin ‘yan sandan na samar da tsaro domin gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci da kwanciyar hankali.
(NAN)
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 41 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com