Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa kananan yara miliyan 14 da dubu 700 a Najeriya galibinsu ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa na cikin hadarin kamuwa da cutar Tamowa wadda karancin abinci me gina jiki ke haddasawa.
Asusu na UNICEF ya bayyana cewa idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, a cikin shekarar dake shirinkarewa, yara miliyan 13 za su fuskanci cutar tamowa yayin da wasu miliyan 1 da dubu 700 kuma za su fuskanci matsananciyar cutar ta Tamowa galibi a yankin arewacin Najeriyar
Asusun na UNICEF ya ce abin takaici ne yadda alkaluma ke nuna mutuwar kananan yara 100 ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa duk bayan sa’a daya a Najeriya, yayin da wasu yaran na daban miliyan 12 ke cikin halin matsanancin rashin abinci.
Read Also:
Shugabar sashen abinci mai gina jiki ta UNICEF a Najeriya Nemat Hajeebhoy, ta ce yara a Najeriya na halin tsananin bukatar abinci mai gina jiki lura da yanayin da kasar ke ciki na tabarbarewar tattalin arzki da ya sanya iyalai gaza samun isasshen abinci.
A cewar jami’ar matsaloli masu alaka da ambaliyar ruwa da ta lalata tarin amfanin gona a sassan Najeriya na shirin sake tsananta karuwar yaran da ke fama da wannan cuta ta rashin isasshen abinci mai gina jiki wato cutar yunwa ko kuma Tamowa.
Nemat Hejeebhoy ta ce za a fuskanci karuwar yara masu fama da matsalar cutar ta Tamowa a 2023 saboda karancin abinci da Najeriya za ta fuskanta mai alaka da sauyin yanayi.
UNICEF ta ce idan har gwamnatoci da sauran wadanda abin ya shafa basu dauki matakan da suka kamata ba, rayuwar kananan yaran masu fama da yunwa na cikin hadarin gaske, kari kan miliyoyin yaran da yanzu haka ke fama da cutar ta Tamowa.
UNICEF
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 5 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 46 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com