Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da ikirarin wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta yi na cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daya daga cikin gwamnoni uku da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta bayyana da boye kudade a gidajensu.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa, hukumar EFCC ba ta lissafa sunayen gwamnonin da take zargi ba, amma jaridar ta bayyana sunan gwamnoni akan karya.
Read Also:
Ya ce rahoton da kafar ta fitar, ba shi da tushe a labaran bincike, sai dai kawai hasashe na mawallafa ko kuma wani yunkuri na bata sunan gwamnan da gangan.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, Gwamna Ganduje bai boye Biliyoyin Nairori a gida ba don biyan ma’aikatan gwamnatinsa albashi, sabida gujewar faduwar banki.
Kwamishinan ya kara da cewa jihar Kano na daya daga cikin jihohin tarayya da ke biyan albashin ma’aikata akan lokaci, a lokacin da da jaridar ta fitar da rahoton karya, an fara ba wasu Ma’aikatan jihar albashin watan Oktoba.
Don haka ya yi kira ga jaridar da ta janye labarin tare da neman gafarar gwamnatin ba tare da bata lokaci ba, gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 8 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 50 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com