Kungiyar Malaman jami’o’I Nijeriya (ASUU) ta kawo karshen taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) inda ta yanke matsayar ba zata sake shiga wani yajin aiki ba.
Sai dai kungiyar ta yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na mayar da malaman jami’o’i kamar ma’aikatan wucin gadi ta hanyar biyansu Rabin albashin su.
Read Also:
A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata bayan kammala taron NEC, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa malaman jami’o’in cikakakkun ma’aikata ne ba na wucin gadi ba.
Ya ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin na watanni takwas a ranar 14 ga Oktoba, 2022 bisa bin umarnin kotun ma’aikata ta kasa da kuma la’akari da kokarin tsoma bakin ‘yan Najeriya masu kishin kasa, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.
Osodeke ya kara da cewa matakin da kungiyar ta dauka alamu ne da suka nuna tsantsar biyayyar ta ga bangaren shari’a, da sauran cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati a kodayaushe da suke kira ga kungiyar data sanya kishin kasa fiye da bukatun kansu.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 27 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 8 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com