Home DUNIYA Burtaniya ta Janye Gargadin Yiwuwar Kai Hari Birni Abuja

Burtaniya ta Janye Gargadin Yiwuwar Kai Hari Birni Abuja

Birtaniya ta janye gargadin da ta yi ga al’ummarta game da yiwuwar hare-haren ta’addanci a babban birnin Najeriya Abuja, inda ta ce a yanzu al’amura sun fara daidaita a birnin saboda daukar matakan kawar da waccan barazana da mahukuntan kasar suka yi.

Makwanni biyu bayan Ofishin jakadancin Birtaniyar ya bi sahun takwarorinsa na Amurka da Italiya wajen gargadin al’ummominsu da ke rayuwa a Najeriya kan su kauracewa ziyartar wasu sassa na kasar musamman birnin Tarayya Abuja game da yiwuwar hare-haren ta’addanci, Ofishin ya yi sake Magana da yayi tun da fari inda ya bayyana cewa yanzu barazanar ta kau a Abuja, sai dai har yanzu babu cikakken tsaro.

Wata sanarwar ofishin kula harkokin ci gaban kasashen renon Ingila na FCDO da ya wallafa a shafinta jiya litinin, ta ce ta janye batun hana al’ummominta bulaguro zuwa Abuja duk da cewa har yanzu akwai barazanar tsaron, sai dai ta ce har yanzu hanin ya na nan kan sauran sassan kasar musamman jihohin arewaci.

Ofishin na FCDO ya sabunta gargadi kan ziyarta jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da kuma Katsina baya ga Zamfara da Delta, da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River wadanda Ofishin ya ce suna fama da barazanar hare-haren ta’addanci .

Sanarwar ta ce bata sauya zani ba, game da barazanar hare-haren ta’addancin da ake fuskanta a jihohin Bauchi da Kano da Jigawa da Neja da Sokoto da Kogi State baya ga wani yanki na jihar Kebbi mai tazarar kilomita 20 da jihar Neja kana jihar Abia sai kuma wasu sassa na jihohin Delta da Bayelsa da Rivers da Pulato da Taraba.

Ofishin ya shawarci matafiya da su rika duba sanarwar hukumomi game da yanayin tsaron yankin kafin kai ziyara yayinda yace mafi dacewa shi ne al’ummomin na Birtaniya su kaucewa zuwa jihohin haka zalika su yi taka-tsan-tsan da ratsawa wata kasa a kokarinsu na komawa gida.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp