Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya na bayyana cewa ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da hakimin gundumar Kwangami a karamar hukumar Zurmi ta jihar tare da wasu mutane 6.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne da manyan makamai a ranar Litinin, inda suka jefa al’ummar kauyen cikin rudani, kuma suka dauke basaraken, Alhaji Muhammad Galadima.
Sun kara da cewa ‘yan ta’addan sun bi wadannan mutane har gidajensu ne suka dauke su.
A waje daya kuma, ‘yan bindiga ssun sako mutane 6 da suka sace a kauyen Kazauda na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara bayan da aka biya Naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa.
Kawo yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba tace ba komai kan wannan batu.












